1 Corinthians 10

Gargaɗi daga Tarihin Israʼila

1Ba na so ku kasance da rashin sani, ʼyanʼuwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku. 2An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku. 3Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda 4suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne. 5Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu koʼina a cikin hamada.

6To, waɗannan abubuwa misalai
Ko kuwa ire-ire; haka ma a aya 11
ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
7Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa: “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”
Fit 32.6
8Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi-har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. 9Kada mu gwada Ubangiji yadda waɗansunsu suka yi-har macizai suka kakkashe su. 10Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har malaʼika mai hallakarwa ya hallaka su. 11Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13Ba jarabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

Bukukuwan Gumaka da Cimar Ubangiji

14Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka. 15Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa. 16Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba? 17Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.

18Ku dubi mutanen Israʼila: Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba? 19To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu? 20Aʼa, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu. 21Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji ku kuma ci a na aljanu. 22Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?

ʼYancin Mai Bi

23“Ana da dama a yi kome”— sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa. 24Kada wani yǎ kula da kansa kawai, sai dai yǎ kula da waɗansu kuma. 25Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yǎ damu da inda abin ya fito, 26gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”
Zab 24.1


27In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yǎ damu da inda abin ya fito. 28Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yǎ kasance babu laifi—  29ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shariʼanta ʼyancina? 30In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?

31Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. 32Kada ku sa wani yǎ yi tuntuɓe, ko Bayahude ne, ko Bahelene ko kuma ikkilisiyar Allah—  33kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.

Copyright information for HauSRK